Edson Arantes do Nascimento, wanda aka fi sani a duniya da suna Pelé, an haife shi ne ranar 23 ga watan oktoba a wata k'aramar gari mai suna Três Corações a Jihar Minas Gerais a K'asar Brasil. Bayan an haife shi, iyayensa sun yi bikin rad'a masa suna da baptisma a wata chochi wadda a ke kira Igreja da Sagrada Familia de Jesus, Maria e José. Mahaifinsa João Ramos do Nascimento ko kuma Dondinho, watau sunan da aka bashi a lokacin zamaninsa shi ma ya buga k'wallon k'afa na rukuni-rukuni. Ya yi babban domin irin gwanintar da ya nuna ta fannin buga k'wallon k'afa; musamman buga k'wallo da kai. Ya yi wasan 'dan tsakiyar fili tare da wata kungiyar k'wallon k'afa mai suna Fluminense har zuwa lokacin da ya sami wata raunin da ya dakatar da shi daga cin gaba da buga k'wallon k'afa a gasar rukuni-rukuni.

Sunan mahaifiyarsa Celeste. Ta girmar da Pelé da sauran 'ya'yanta cikin kyakyawar tarbiya da soyaya mai yawa.

A lokacin da ya ke yaro k'ank'ani, Pelé da iyayensa sun k'aura zuwa wani gari mai suna Baurú a tsakiyancin jihar São Paulo a k'asar Brasil. A wannan garin ne ya fara koyan hikimar wasan k'wallon k'afa (a harshen Portugal-Brasil, watau futebol), har ya gwanance. Shi da kansa ya ta'ba cewa "tinha três corações" fassaran wannan karin magana shi ne wai ya na da zuchiyoyi guda uku. Ya na magana ne a kan garuruwa guda uku da ya rik'e mafi kusa da zuchiyarsa watau garin da aka haife shi, Três Corações, da birnin Baurú da kuma Santos.

Sana'o'in Pelé

Da farko dai sana'ar da Pelé ya fara yi, shu shaina ne watau mai goge takalma. Amma ya na sha'awar buga k'wallon k'afa har cikin mafarkinsa

Pelé ya fara buga k'wallon k'afa tun yana kurchiyarsa. Bayan da ya yi wasa da wa'dansu k'ananan k'ungiyoyin k'wallo kamar su Baquinho da kuma Sete Setembro, ya kuma fara buga k'wallon k'afa a wata kulob mai suna Ameriquinha. Wannan kulob ba ta da kwatch (watau mai horan 'yan wasa). A wannan lokacin ne fa, yana da shekaru goma sha 'daya kawai, kuma wani shahararan 'dan buga k'wallo na k'asar Brasil mai suna Waldemar de Brito ya ga irin basira da k'ok'arin da Pelé ya nuna a wasar k'wallon k'afa. De Brito ya gane cewa lallai ya kamata ya gayyaci wannan matashi zuwa k'ungiyar k'wallon k'afa wanda shi De Brito ke neman ya fara. (Sunan k'ungiyar Clube Atlético Baurú?) A 1956, Pelé ya cika shekaru goma sha biyar da haihuwa a duniya. A lokacin ne kuma de Brito ya gayyace shi zuwa babban birnin São Paulo domin gwadawar wasan k'wallo na a tsinto a fitar domin shiga k'ungiyar wasan k'wallo mai muhiminci wanda ake kira Santos Futébol Clube (SFC). Rannan da ya fara wasa, de Brito ya fad'a wa masu horan yan wasa a wannan k'ungiyar cewa "wannan yaro (watau Pelé) zai zama babban zakaran cikin k'wararun 'yan buga k'wallon k'afa a duk duniya nan gaba".

Babbar ranar wasan k'wallo na farko ta taho wa Pelé ne ranar 7 ga watan Satumba 1956. An zab'i Pelé ya buga k'wallo a madadin wani 'dan wasan tsakiyar fili mai suna Del Vecchio. Da shigowarsa filin wasa, sai ya buga k'wallo har cikin raga, wadda ta zama k'wallo na shidda cikin bakwai da k'ungiyar Santos ta zuzura wa abokiyar karawarta da ci 7-1. Pelé ya buga k'wallo a raga ne a minti na talatin da shidda cikin loton wasa tsakanin Raimundinho da Tite. Pelé ya sami k'wallon a lokacin da ya ke kewaye da 'yan tsaron fili amma da ya buga k'wallon, abin al'ajibi da mamaki ya faru watau sai da k'wallon ta wuce a k'ark'ashin jikin mai tsaron gida watau gwalkifa mai suna Zaluar, har k'wallo ta shiga raga. To, a wannan rana ne fa Zaluar ya yi suna, domin shi ne gwalkifa na farko da Mai Girma Pelé ya samu nasarar buga masa k'wallo, ta k'ure shi har cikin raga.

Ba shakka nan da nan ne Pelé ya fara yin suna mai tagomashi ta fannin buga k'wallon k'afa. A farkon wasan rukuni-rukuni da Pelé ya buga wa k'ungiyar Santos, ya kasance cewa Pelé ya buga zunzurutun k'wallaye har guda hu'du cikin raga.

Shekara mai zuwa ya kasance 'dan wasa mai fara buga wasa, ya samo wa k'ungiyarsa nasarar cin k'wallaye har guda talatin da biyu. Domin haka ne fa ya zama 'dan wasa mai muhimmincin gaske a rukunin jiha na São Paulo.

An yi wa k'ungiyar Corinthians ta'a'di

Cikin shekaru goma da Pelé ya yi tare da k'ungiyar k'wallon k'afa ta Santos, wata abokiyar karawar Santos mai suna Corinthians do Parque de São Jorge, ba ta sami daman cin nasara a gasar rukuni-rukuni ko sau 'daya ba. Ga sakamakon wasanni da a ka buga tsak'annin k'ungiyar Santos da k'ungiyar Corinthians, da kuma k'wallayen dalla-dalla.

Ranar 14 ga watan Satumba, 1958 - Santos ta sha Corinthians da ci 1-0. Pelé ne ya jefa wannan k'wallon a raga.
Ranar 7 ga watan Disamba, 1958 - Santos ta gigice Corinthians da zunzurutun k'wallaye har guda 6-1. A nan ma Pelé ne ya buga k'wallaye hudu cikin guda shidda 'din.
Ranar 30 ga watan Afrilu, 1959 - Santos ta ci Corinthians da k'wallaye 3-2. Pelé ya jefa k'wallo guda a raga.
Ranar 26 ga watan Agusta, 1959 - Santos ta k'ara maimaita nasararta da ci 3-2. A nan ma Pelé ya buga k'wallo guda a raga.
Ranar 27 ga watan Disamba, 1959 - Santos ta yi wa Corinthians yankan k'auna da ci 4-1. Pelé ya jefa k'wallaye biyu a raga.
Ranar 31 ga watan Yuli, 1960 - Santos da Corinthians sun sami kunnen doki da ci 1-1. Pelé ya jefa k'wallo guda a raga
Ranar 30 ga watan Nuwamba, 1960 - Santos ta yi lu'bus da k'ungiyar Corinthians da ci 6-1. Pelé kuma, ya jefa k'wallo guda a raga.
Ranar 3 ga watan Disamba, 1960 - An maimaita wasan kunnen doki da ci 1-1
Ranar 23 ga watan Satumba, 1962 - Santos ta rikita Corinthians da ci 5-2. Pelé ya jefa k'wallaye biyu cikin raga.
Ranar 3 ga watan Nuwamba, 1962 - Santos ta sha Corinthians da ci 2-1. Nan ma Pelé ya jefa k'wallo guda a raga.
Ranar 3 ga watan Maris, 1963 - Santos ta lashe Corinthians da ci 2-0. Duk k'wallayen biyu, Pelé ne ya jefa su a raga.
Ranar 21 ga watan Satumba, 1963 - Santos ta sami nasara da ci 3-1. Nan kuma, duk k'wallayen guda uku, na Pelé ne.
Ranar 14 ga watan Disamba, 1963 - Santos da Corinthians sun sami kunnen doki 2-2. Pelé bai yi wasa a wannan gasar ba.
Ranar 18 ga watan Maris, 1964 - Santos ta zuba wa Corinthians ruwan sanyi da ci 3-0. A yau, Pelé ya buga k'wallo guda a raga.
Ranar 30 ga watan Satumba, 1964 - Santos da Corinthians sun kuma sami kunnen doki 1-1. Pelé ya buga k'wallo guda.
Ranar 6 ga watan Disamba, 1964 - Santos ta yi wa Corinthians mumunar 'barna da ci 7-4. Pelé ya zura k'wallaye guda hudu.
Ranan 29 ga watan Agusta, 1965 - Santos ta ci Corinthians da k'wallaye 4-3. Pelé ya buga k'wallaye biyu a raga.
Ranar 14 ga watan Nuwamba, 1965 - Santos ta sha Corinthians da ci 4-2. Pelé ya buga k'wallo guda a raga.
Ranar 8 ga watan Oktoba, 1966 - Santos ta k'ara yi wa Corinthians yankan k'auna da ci 3-00.
Ranan 17 ga watan Disamba, 1966 - Santos da Corinthians sun k'ara sami kunnen doki 1-1. Pelé bai yi wasa a wannan ranar ba.
Ranan 13 ga watan Mayu, 1967 - Nan ma an maimaita samun kunnen doki da ci 1-1. Pelé ya buga k'wallo guda a raga.
Ranan 10 ga watan Satumba, 1967 - Santos ta sha Corinthians da ci 2-1. Pelé bai buga wasa a wannan ranar ba.
Ranan 10 ga watan Disamba, 1967 - Santos ta ci Corinthians da ci 2-1. Pelé ya buga k'wallo guda a raga.

Hak'ik'a sai bayan kusan shekaru goma, a ranar 6 ga watan Maris 1968 ne k'ungiyar Corinthains ta sami ikon k'watan kanta da k'yar daga hannun Santos inda ta sha Santos da ci 2-0.

Ba da da'dewa ba bayan lokacin wasan rukuni-rukuni na farko da Pelé ya buga tare da k'ungiyar SFC, sai wani mai horan k'ungiyar 'yan wasa na k'asar Brasil baki 'daya watau "kwatch" mai suna Sylvio Pirrilo ya gayyaci Pelé ya shiga shahararan k'ungiyar wasa ta k'asar Brasil.

Pelé ya fara buga k'wallan k'afa tare da k'ungiyar k'asar Brasil ga baki d'aya ranar 7 ga watan Yuli a 1957, yana da shekaru goma sha shida da haihuwa. A wannan rana, 'yan wasan k'asar Arjantina (Argentina) sun sha k'asar Brasil da ci 2-1. A nan ma Pelé ne ya buga wannan k'wallo guda a raga.

A 1958, lokacin da gasar cin Kwaf na Duniya (World Cup) ta zagayo, duniya baki 'daya ta ambaci wannan "Bak'in Murzani" d'in.

Pelé ya nuna hikima da k'wazo, da saurin gudu, da kuma gwaninta a wasar k'wallon k'afa a wannan gasar. A nan fa sai da bakin kowa ya bu'du domin irin abin al'a'jibi da mamaki da suka gani. Kai! In fa muddun ya shigo filin wasa, jama'a makil na fara ihu da kuwwa na jin da'di tare da nisha'di domin ganinsa. Wannan ya sa har 'yan jaridan k'asar Faransa sun na'da masa rawanin girma na k'asaita wai shi ne "Sarki" a 1961, a sanadin wasan k'wallon da Pelé ya buga tare da SFC a k'asashen Turai.

Pelé A Gasar Cin Kwaf Na Duniya (World Cup)

Pelé ya yi wasa a gasar cin Kwaf na Duniya daban-daban sau hu'du. Da farko dai, ya buga k'wallo a k'asar Sweden a 1958, da k'asar Chile a 1962, da k'asar Ingila a 1966 da kuma a k'asar Meksiko a 1970. Ya ha'da k'wallaye 12 a raga a cikin wasanni 14.

A K'asar Sweden 1958

Wasar na fari da Pele ya buga cikin wannan gasar Kwaf na Duniya ita ce shiga ta uku da k'asar Brasil ta yi. A wannan lokaci, 'yan wasan k'asar USSR sun yi wasa da k'asar Brasil. An sa Pelé a filin wasa na Kwaf na Duniya domin rok'on da manyan 'yan wasa k'ungiyar Brasil suka yi. Bugu da k'ari kuma, sun yi rok'o wai don Allah Vincente Feofe ya tabbatar cewa a sa Pelé tare da wani 'dan wasan k'asa na Brasil mai suna Garrincha a fili a lokaci d'aya. Sun yi wannan rok'o d'in bayan wasan karo na fari inda Brasil ta lashe k'asar Austria da ci 3-0, kuma bayan k'asar Brasil ta kara da k'asar Ingila, inda a ka sami kunnen doki da wasa babu ci ko 'daya, watau 0-0.

A karawar da aka yi tsakanin k'asar Brasil da k'asar USSR Pelé bai buga k'wallo a raga ba, amma Brasil ta yi ma k'asar Rasha 'barna da ci 2-0. Wani 'dan wasa mai suna Vavá ne ya buga duk k'wallayen guda biyu a raga. A wasan zagaye na biyu, Pelé ne ya buga k'wallo guda 'daya wanda Brasil ta lashe abokiyar karawarta.

A karawar wasa na kusa da na k'arshe tsakanin k'asar Faransa da k'asar Brasil, an zuzzura wa k'asar Faransa zunzurutun k'wallaye har guda biyar. In da Brasil ta samu ci 5-2. Didi da Vavá sun buga k'wallo guda-guda a raga kowannensu.

A karo na k'arshe, Brasil ta kara da k'asar Sweden, inda ta yi wa k'asar Sweden yankan k'auna da ci 5-2. Pelé ya buga kwallaye biyu a raga (nan fa sai a duba hoton bidiyo) Vavá ya buga k'wallaye biyu, kuma wani 'dan wasa mai suna Zagalo shi ma ya buga k'wallo guda a raga. Ta wannan hanya ne Brasil ta sami ci 5-2.

A K'asar Cile (Chile) 1962

Tun daga farkon wasa da k'asar Brasil ta buga da k'asar Meksiko,nan da nan, sai Pelé ya buga k'wallo a raga. Da wannan k'wallo guda rak Brasil ta mamaye k'asar Meksiko. Allah bai sa kwaf d'in ya zama na Pelé ba domin ya kasa cin gaba da wasa bayan wata muminar rauni da ya ji a k'afa yayin da ya buga wasan minti goma da k'asar Cakwaslabakiya (Czechoslovakia). Daga nan, kwaf d'in ya zama na Mané Garrincha. A lokacin kuma, an sa wani 'dan wasa mai suna Amarildo ya buga k'wallo a maimakon Pelé.

A K'asar Ingila 1966

A wannan gasar cin Kwaf na Duniya, Brasil ba ta maimaita irin tarihin sa'a da ta saba yi ba. K'asar Brasil ta gayyaci 'yan wasa 43.

A lokacin da zasu yi tafiya k'asar Turai, sai a ka fitar da k'wararun 'yan wasa guda biyu daga gasar gaba d'aya. Wadanda a ka cire sun had'a har da mai tsaron gida watau gwal kifa mai suna Valdir da wani 'dan wasan tsakiyar fili mai suna Servílio.

A zagaye na fari, Brasil ta mamaye k'asar Bulgariya da ci 2-0. Pelé da Garrincha ne suka buga k'wallo guda-guda ko wannensu. Da a ka kara da k'asar Hangariya, an sha Brasil da ci 3-1, kuma a wasa mabiyin wannan da aka buga da k'asar Fortugal, an fitad da Pelé daga wasa sau biyu, domin raunanukan da ya ji a filin wasa, sai aka hana shi wasa baki d'aya.

A K'asar Meksiko 1970

Cikin wannan gasa ne kasar Brasil ta d'auki kwaf na Jules Rimet ta ajiye ta a gida. Da farko dai Brasil ta yi lub'us da k'asar Cakwaslabakiya (Czechoslovakia), inda Brasil ta samu ci da kwallaye 4-1. Wad'anda suka buga kwallayen nan guda hu'du sun ha'da har da Jairzinho wanda ya buga guda biyu, Pelé da Rivelino kuma sun buga k'wallo guda-guda a raga. 'Yan Ingila sun zama mabiyin sawun 'Yan Cakwaslabakiya, watau Brasil ta sha su da ci 1-0, wanda Jairzinho ne ya buga

A karawar da Brasil ta yi da k'asar Romaniya. An lashe k'asar Romaniya da ci 3-2. A nan ma, Pelé ya buga k'wallaye biyu a raga, shi kuma Jairzinho ya buga k'wallo guda a raga.

Bayan haka, Brasil ta gigice k'asar Peru da ci 4-2.

A wasan dab da na k'arshe, k'asar Urugwai (Uruguay) ta sha kashi a hannun Brasil watau Brasil ta mamaye ta da ci 3-1.

Da a ka buga wasa ta k'arshe, Brasil ta kara da abokiyarta k'asar Italiya (Italy) watau Brasil ta rinjayi k'asar Italiya da ci 4-1. Ga sakamakon wadanda suka samo wannan nasarar. Pelé ya buga k'wallo guda a raga (nan ma sai a duba hoton bidiyo); Gérson, Jairzinho da Carlos Alberto su ma sun buga k'wallo guda-guda ko wannensu.

A gasar cin wannan kwaf, Pelé ya yi suna domin "k'walaye na kusa da gaske" guda uku da ya buga, irin wad'anda ba a ta'ba gani ba a tarihin buga k'wallon k'afa.

A wannan lokaci ne kuma mai tsaron gida watau gwalkifa mai suna Banks na k'asar Ingila ya zama sananne a lokacin da ya chabke wata k'wallo da Pelé ya daka masa da kai.

Shekaru Uku Tare Da K'ungiyar K'wallo Mai Suna New York Cosmos

"Farawan wannan labari shi ne a 1971 lokacin da na ke tare da k'ungiyar Santos FC, mun yi wasa a birnin Kingston a k'asar Jamaica. Anan wa'dansu manyan bak'i suka kawo mini ziyara. Bak'in sun ha'da har da wani mai suna Clive Toye Janar Manaja na wata sabuwar k'ungiyar k'wallon k'afa mai suna Cosmos, a babban birnin New York a k'asar Amirka. Ya taho ne tare da Phil Woosnan wanda ya zama mai halartar k'ungiyar NASL, da kuma Kurt Lamm Sakatare Janar na hukumar k'ungiyoyin k'wallon k'afa a k'asar Amirka (U.S. Soccer Federation). Dalilin zuwansu shi ne wai su na so in sanar da su ko ina so in je k'asar Amirka in buga wa k'ungiyar Cosmos k'wallo bayan na yi murabus daga k'ungiyar Santos.

Ferfesa Mazzei ne ya fasara mini nufin maganarsu, amma sai na amsa na ce "Ferfesa, ka gaya musu wai sun fita daga hankalinsu! Ni fa bayan Santos ba zan ta'ba buga wa wata k'ungiya k'wallo ba."

Shekaru uku bayan wannan ziyara, ranar da na buga wasata ta k'arshe wa k'ungiyar Santos, sai shi Clive Toye ya buga mini waya daga birnin New York cewa k'ungiyar Cosmos na buk'atar magana da ni game da ba ni kwantiragi na wasa.

Mun yi watanni shida ana ja ni in ja ka da wannan al'amari. Cikin wannan lokaci kuma, na sadu da su a wurare daban-daban a duniya, kuma sun rubuto mini wasik'u da yawa. Daga baya dai sai na yarda da maganar Warner Communications, shi ne maigidan New York Cosmos. A haka ne na yarda in dawo rayin rukuni-rukuni in buga musu k'wallo har shekaru uku.

Pelé: Mutumin Da Ba Za'A Ta'ba Manta Da Shi Ba

Pelé wani irin mutum ne mai iya jawo jama'a da yawa. A k'arshen shekaru na 1960-1969, lokacin da Pelé ya ke buga k'wallo tare da k'ungiyar Santos, ya ziyarce k'asar Nijeriya domin buga k'wallon sada zumunta. Idan an tuna, a wannan lokaci ne k'asar Nijeriya ke gwabza yak'in basasa da 'yan a dawa. Abin mamaki shi ne yak'in ya tsaya tsak cikin kwannakin da ya ke ziyara.

Zuwansa k'asar Amirka, a yayin da ya ke buga wa k'ungiyar Cosmos k'wallo, mutane masu 'dimbin gaske na fitowa k'wansu da kwarkwatansu zuwa dandalin wasa domin su kalle shi ya na buga k'wallo. Pelé ya yi suna a da da kuma a yanzu cikin duniya gaba daya domin yadda mutane suka k'aunace shi domin gwanintarsa ta fannin buga k'wallon k'afa.

Shahararrun marubuta da mutane kalakala sun fa'di karin magana iri-iri a kan Pelé, ga misalai nan:

"'Yaya a ke rubuta sunan Pelé?' S-A-R-K-I."
Jaridar Sunday Times ta birnin London, a k'asar Ingila

"Da ba a haifi Pelé mutum ba, ashe da an haife shi k'wallo."
Armando Nogueira, 'dan jarida a Brasil.

"Buga k'wallaye dubu a raga kamar Pelé ba abin wuya ba ne, amma buga k'wallo guda kamar irin na Pelé shi ke da wuya ne."
Carlos Drummond de Andrade, Marok'i a Brasil.

"Bayan ya buga k'wallo na biyar a raga na so in tafa masa."
Sigge Parling, mai tsaron fili na k'asar Sweden a gasar Cin Kwaf na Duniya a 1958.

"Ina zaton wai Pelé mutum ne mai jini da tsokan jiki kamar ni, amma ashe na yi kuskure da zaton haka."
Tarciso Burnigch, 'dan tsaron gida na k'asar Italiya lokacin da Pelé ya yi wasan k'arshe a gasar cin Kwaf na Duniya a 1970.

"Kai, mutumin nan! Ka yi suna!"
Robert Redford, bayan ya ga mutane da yawa suna neman alamar rubutun sunan Pelé, amma ba wanda ya nemi tasa.

"Sunan Pelé ba zai ta'ba mutuwa ba."
Edson Arantes do Nascimento - Pelé.

A 1993, an rubuta sunan Pelé a wani shahararan wuri wanda ake kira "United States Soccer Hall of Fame" inda a ka rubuta sunayen wad'anda suka yi suna a wasan k'wallo.

Bayan Pelé ya buga k'wallo a birnin Lima a k'asar Peru, an mak'a wata rubutu a jikin bangon da ya kewaye filin wasa. Rubutun ta na ce wa "Pelé ya ta'ba buga k'wallo a wannan filin wasa."

Pelé ya ta 'ba dakatar da yak'i har tsahon kwanaki biyu lokacin da ya ziyarci k'asar Nijeriya dab da yak'in basasa. Hafsoshin sojojin Nijeriya da 'yan a dawan Biafra sun sa hannu a wata yarjejeniya inda suka yarda a dakatar da yak'in domin jama'a su samu zuwa filin wasa su ga Pelé.

Ranar 18 ga watar Yuli 1971, Pelé ya yi murabus daga k'ungiyar k'wallo ta k'asar Brasil. Kimanin mutane dubu 'dari biyu (200,000) ne suka hallara a filin wasa a Maracanã a ranan, domin su ga wasarsa ta k'arshe, su kuma nuna ba'kin cikinsu domin zakaransu zai yi rataya.

A ranar, Pelé ya bayar da taguwarsa mai alamar lamba goma wanda ya saba sanya wa idan zai buga k'wallo ga wani yaro mai shekaru goma.

Pelé ne kawai 'dan wasan k'wallo wanda ya samu shiga gasar cin Kwaf na Duniya daban-daban har sau uku a 1958 da 1962 da kuma 1970. Lissafi ta nuna cewa ya buga k'wallaye 1,281 (ko 1,284) har cikin raga a wasanni 1,363. Wannan ya fi duk 'yan wasa a tarihin wasan k'wallon k'afa.

Dalla-dalla dai, ya buga kimanin k'wallo 0.93 a cikin kowanne wasa da ya shiga.

A 1959, lissafi ta nuna cewa ya buga k'wallaye 126 a wasan rukuni-rukuni na "Paulist" (na São Paulo) a shekara guda kawai, fiye da kowa cikin tarihi. Ranar 21 ga watan Nuwamba, 1964 Pelé ya samu nasarar buga k'walaye har guda takwas a raga, a cikin wasa guda 'daya kawai, in da a ka yi wa k'ungiyar Botafogo na Rio de Janeiro yankan k'auna.

Ranar 19 ga watan Nuwamba 1969, Pelé ya samu buga kwallo na cika k'irgen dubu 'daya a wata "fenalti kik" cikin minti na 34 da fara wasa da a ka buga da k'ungiyar Vasco da Gama. Nan Pelé ya ce "Para as Criancinhas Pobres do Brasil" Watau ya ce, ya bayar da wannan kwallo zuwa ga yara, da talakawa da tsofafi, da gajiyayu da kuma fakirai na k'asar Brazil.

Pelé yana 'daya daga cikin 'yan wasan da suka bunk'asa wasan k'wallo na "Shekarun Ganin Kyallin" Kwaf na Liberatadores daga 1960 zuwa 1963. Cikin wannan lokaci wata shahararan k'ungiyar k'wallo ta k'asar Uruguay mai suna Peñarol ta kara a wasa na karshe da k'ungiyar Santos.

Peñarol ta ci nasarar samun wannan kwaf 'din a 1960 da kuma a 1961, Santos ta kuma 'dauki kwaf 'din har tsahon shekaru biyu.

Pelé ya zama 'dan masanin buga k'wallon k'afa na tsakiyar fili, ya zama zakaran wak'ilai na k'wararrun 'yan wasa da k'asar Brasil ta ta'ba samu, kamar su Vavá, Didi, Garrincha da sauransu. Ra'a'yin jama'a da yawa ne wai Pelé ya na iya buga k'wallo a duk inda aka sa shi wasa a filin k'wallon k'afa.

Akwai lokacinda ya tab'a gaya wa manajan Santos a sa shi 'dan tsaron gida watau gwalkifa. Gwadawarsa ta iso ranar 19 ga watan Janairu 1964, an sa Pelé ya yi aikin tsaron gida cikin wasa na dab da na k'arshe a gasar cin Kwaf na K'asar Brasil a madadin gwalkifa mai suna Gilmar wanda aka fitar da shi daga wasa.

Bayan ya buga k'wallaye uku a raga, P elé ya sa taguwa mai lamba 1 har tsahon minti biyar. Cikin wannan lokaci ne Pelé ya yi wa k'ungiyarsa aikin agaji har Santos ta sami nasarar shiga karawa na k'arshe.

Bankwana da Santos

Pelé ya buga wa Santos Futebol Clube wasarsa ta k'arshe a tsahon minti 21 ranar 3 ga watan Oktoba, 1974 da k'arfe 9:08 na yamma. Santos ta lashe Ponte Preta da ci 2-0. Cláudio Adão da Geraldo ne suka buga wadannan k'wallayen a raga. Amma gasar ta k'are wa jama'a da 'yan kallo lokacin da...

"Aos 21 minutos de jogo, quando Pelé, inesperadamente, pegou a bola com as mãos, ajoelhou-se no meio do gramado e ergueu os braços, a torcida que estava em Vila Belmiro não pôde negar-se a um momento de surpresa. Mas, foi apenas um momento. Logo, ela compreendeu que Pelé estava determinando o final de sua carreira de maior jogador de futebol de todos os tempos"

[A minti na 21, lokacin da Pelé ya d'auki k'wallo a hannayensa biyu, sai ya tsugunna a tsakiyar filin wasa ya d'aga hannayensa sama, 'yan kallo a filin wasa na Vila Belmiro sun yi 'dan sha mamaki na minti guda. Amma na minti guda kawai ne. Nan da nan sai jama'a suka gane cewa Pelé ya na yi musu bankwana ne domin a ranar zai yi murabus daga wasan k'wallon k'afa, ya zama zakaran k'wararrun 'yan wasan k'wallon k'afa.]

Wannan ne k'arshen sana'a'r buga k'wallo da Pelé ya yi tare da taguwar Santos mai zane. Bayan haka, Pelé ya je k'asar Amirka inda k'ungiyar Cosmos na birnin New York ta gayace shi domin bunk'asa wasan kwallon k'afa a k'asar. Idan akwai abu guda da Pelé yake da ikon yi, wannan zai zama iya kawo wa duk al'amarin da ya sa hannu suna, domin girmansa da hikimarsa da muhimminci da ya ke da shi a duniya.

 

guestbook.jpg (6475 bytes)guestbook_text.jpg (7936 bytes)

       

 
digits.net
www.digits.net
7/1996